Home HAUSA KORAFI: PDP Ta Daukaka Kara A Kan Tsadar Tikitin Zaben Kananan Hukumomi...

KORAFI: PDP Ta Daukaka Kara A Kan Tsadar Tikitin Zaben Kananan Hukumomi A Kano

416
0
SHARE

Jam’iyyar PDP reshen jihar Kano ta shigar da Korafin ta gaba kotun Daukaka Kara akan tsadar tikitin neman takarar kujerun Kananan hukumomi, wanda za a gudanar da zaben a ranar 10 ga watan Fabrairun 2018.

Shugaban jam’iyyar Sanata Mas’ud El-Jibril Doguwa, ya bayyanahaka ga  manema labarai, ya ce wannan korafi ya zama wajibi ne domin ceto dimokuradiyya da kuma tsarin siyasar Nijeriya.

Doguwa ya tuhumi jagorancin gwamnatin APC a jihar da sanya tsada akan tikitin neman takarar, wanda a cewar sa idan aka sa musu ido zasu ci-gaba da gurbata tsarin siyasa da yiwa dimokuradiyya karan tsaye.

Ya kuma bayyana damuwar sa akan  tsadar takardun neman takara, duba da irin wahalhalun rayuwa da gwamnatin APC ta jefa al’ummar Nijeriya.

Leave A Comment