Home HAUSA Raddi: Dan Takarar Shugaban Kasa Na Jam’iyyar PT Ya Kalubalanci Gwamnatin APC

Raddi: Dan Takarar Shugaban Kasa Na Jam’iyyar PT Ya Kalubalanci Gwamnatin APC

50
0
SHARE

Dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PT Gbenga Olawepo-Hashim, ya kalubalanci jam’iyyar APC game da yadda ta haddasa wa miliyoyin ‘yan Nijeriya fatara da talauci.

A cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai, ya ce maimakon gwamnatin APC ta assasa wa mutane arziki da yalwa, ya ce mutane miliyan 88 na cikin kuncin talauci da fatara.

Ya ce a cikin watanni hudu da su ka gabata zuwa yau, mutane sama da miliyan daya su ka afka cikin kangin fatara, ga kuma tsadar kayan masarufi da ta yi wa kasuwannin Nijeriya dabaibayi.

Hashim ya cigaba da cewa, gwamnatin APC ba ta iya tafiyar da tattalin arziki yadda zai kara samar da yalwa a cikin kasa ba, ya na mai nuna rashin jin dadin yadda matasa marasa aikin yi ke ta kara yawa a kasar nan.

Leave A Comment