Home HAUSA RIKICIN BENUE: Majalisa Ta Umurci Ibrahim Idris Ya Roki Gafarar Ortom

RIKICIN BENUE: Majalisa Ta Umurci Ibrahim Idris Ya Roki Gafarar Ortom

236
0
SHARE

Majalisar Wakilai ta umurci shugaban rundunar ‘yan sandan Nijeriya Ibrahim Idris ya roki gafarar Gwamnan Jihar Benue Samuel Ortom bisa ikakarin sa na cewa gwamnan mutum ne da ke nitsewa.

 

An dai bada umurnin ne a ranar Larabar da ta gabata, bayan kwamitin kula da harkokin ‘yan Sanda na Majalisar ya gabatar da sakamakon binciken shi.

 

Akasarin ‘yan Majalisar dai sun yi tir da furucin na shugaban ‘yan sanda, inda su ka bukaci a sauke Mashood Jimoh a matsayin mai magana da yawun Hukumar domin daga bakin sa furucin ya fito.

 

Rikicin Benue dai ya haddasa cece-ku-ce a tsakain al’umma, lamarin da ya sa Majalisar ta bukaci Kwamitin da sauran Jami’an Tsaro su yi cikakken bincike a kai.

Leave A Comment