Home HAUSA Ta’addanci: Saurayi Ya Kashe Mahaifiyar Sa A Jihar Edo

Ta’addanci: Saurayi Ya Kashe Mahaifiyar Sa A Jihar Edo

59
0
SHARE

Rahotanni na cewa, wani matashi dan shekaru 21 ya hallaka mahaifiyar sa ta hanyar shake ta, yayin da ta ke barci sannan ya yi wa gawar ta fyade a jihar Edo.

Lamari dai ya afku ne a gidan da mahaifiyar yaron ke haya a garin Ologbo da ke karamar hukumar Ikpoba-Okha ta jihar Edo

Mai laifin Samuel Emobor, ya kashe mahaifiyar sa mai suna misis Christiana Ighoyiwi ‘yar shekaru 58 ne yayin da ya tarar ta na barci.

Kakar yaron Christiana Gabriel ce ta gano lamarin, bayan ta je gidan domin gayyatar ta zuwa wajen bautar su a wani coci da ke kusa da gidan da misalin karfe 6 na safe.

Yaron da ya nemi tsarewa, inda bayan kakar ta yi Ihu makwabtan su su ka kamo shi, daga baya su ka mika shi ga ofishin ‘yan sanda na garin Ologbo.

 

 

Leave A Comment