Home HAUSA Ta’addanci: ‘Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Ma’aikata 8 A Osun

Ta’addanci: ‘Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Ma’aikata 8 A Osun

41
0
SHARE
'Yan Bindiga

Wasu gungun ‘yan bindiga sun yi awon gaba da wasu ma’aikatan kwalejin kimiyya da ke garin Esa-Oke na jihar Osun kamar yadda rahotanni su ka bayyana.

Kakakin kwalejin Adewale Oyekanmi ya bayyana wa manema labarai haka a garin Osogbo, inda ya ce baya ga sace ma’aikatan su takwas, ‘yan bindigar sun kuma halaka wani daga cikin su da ke kokarin tserewa.

Ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 4:30 na ranar Talatar da ta gabata, yayin da ‘yan bindigar su ka tare hanyar Esa-Oke su na tare motoci, ciki kuwa har da ma’aikatan makarantar, sannan su ka yi awon gaba da su.

Sai dai ‘yan bindigar ba su tuntubi iyalan ma’aikatan ko hukumar makarantar ba har yanzu, amma jami’an hukumar tsaro ta DSS, da na kungiyar OPC sun shiga farautar su a dazuzzukan yankin domin ceto ma’aikatan.

Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Osun Folashade Odoro, ta ce ‘yan sanda na sane da lamarin, kuma za su gabatar da jawabi a hukumance nan ba da jimawa ba.

Leave A Comment