Home HAUSA Tattakin Ashura: Kungiyoyi 22 Sun Bukaci Buhari Ya Haramta Addinin Shi’a A...

Tattakin Ashura: Kungiyoyi 22 Sun Bukaci Buhari Ya Haramta Addinin Shi’a A Nijeriya

162
0
SHARE

Wasu kungiyoyin fararen hula da masu zaman kan su, sun bukaci shugaba Muhammadu Buhari ya harmta addini ko akidar shi’a gaba daya a Nijeriya.

Kungiyoyin, wadanda su ka kira taron manema labarai a Abuja, sun yi wa ‘yan siyasa kakkausan kashedi game da siyasantar da harkar tsaron Nijeriya, musamman ganin cewa zabubbukan shekara ta 2019 na ta kara karatowa.

A cikin wani jawabin bayan taro da su ka raba wa manema labarai, kungiyoyin sun bukaci majalisar dinkin duniya ta shiga maganar, domin taka wa kasar Iran da ta ce ta na taimaka wa ‘yan shi’ar da makamai birki.

Leave A Comment