Home HAUSA YAKI DA BOKO HARAM: Hukumar Soji Ta Maida Wa Gwamna Shettima Martani

YAKI DA BOKO HARAM: Hukumar Soji Ta Maida Wa Gwamna Shettima Martani

675
0
SHARE

Ministan Tsaro da wasu manyan jami’an tsaro, sun bayyana takaicin su game da ikirarin da Gwamna Kashim Shettima na jihara Borno ya yi, cewa Sojojin kudancin Nijeriya ne su ka fi bada gudunmawa wajen yaki da Boko Haram.

 

Gwamnan dai ya yi furucin ne a wani taron jin ra’ayoyin jama’a  da Gwamnatin Tarayya ta shirya a Maiduguri, inda ya bada misali da Manjo Janar Rogers Nicholas a matsayin wanda ya bada gagarumar gudunmuwa.

 

Yayin da ya ke maida wa gwamnan martini, Ministan Tsaro, Mansur Dan-Ali ya ce akwai sauran manyan jami’an tsaro da su ka taka muhimmiyar rawa wajen yaki ta ta’addanci.

 

Furucin gwamnan dai, ya janyo cece-ku-ce tsakanin jami’an sojin Nijeriya.

 

Wani jami’in sirri na soji da ya nemi a sakaya sunan sa, ya ce abin takaici ne a ji irin wadannan kalamai daga bakin Gwamna, don hakan ba zai yi wa sojojin da su ka sadaukar da rayuwar su wajen yaki da ta’addancin dadi ba.

Leave A Comment